Yan Sanda Za Su Binciki Wasu Yan Karota Kan Batan Kudin Wani Lauya A Cikin Motar Da Suka Dauka

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta tabbatar da karbar korafin wani lauya mai suna, Barista Ahmad Sani Bawa, inda yake zargin wasu jami’an hukumar Karota da dauke motarsa ba tare da saninsa ba, sannan suka sace masa kudi naira dubu 950.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna, ya ce za a gaiyaci dukkan wadanda lamarin ya shafa don gudanar da cikakken bincike, bisa umarnin kwamishinan yan sandan jihar , CP Ibrahim Adamu Bakori, don gaiyato wadanda ake korafin.

Tunda fari lauyan mai suna Barista A.S.Bawa, ya ce ya ajiye motarsa bisa ka’ida amma ya zo ya tarar batanan,  kuma bayan ya ganota a ofishin Karota ya tarar babu kudinsa naira dubu 950 da kuma wani agogo mai tsada da har yanzu  ba a kiyasta kudinsa ba.

Barista A.S. Bawa , ya kara da cewa bai ga dalilin da jami’an hukumar za su dauke motarsa ba, ba tare da sun ajiye wani da zai sanar da shi ba.

Ya kuma ce yin hakan zai sanya idan mutum yana da ciwon hawan jini zai iya tashi sakamakon damuwa da aka iya zuwa lokaci daya.

Lauyan ya yi zargin jami’an sun sace mosa motar baya ga zargin cin zarafinsa da suka yi.

Haka zalika hukumar karota ta jihar Kano, ta bakin mai magana da yawunta, Abubakar Ibrahim, ya tabbatar da karbar takaddar korafin da aka kai mu su daga rundunar yan sandan jihar.

Sai dai ya ce hukumar su tana da hurimin bincikar ababen hawa, amma ya ce sakamakon bincike da rundunar yan sandan zata yi ba za su ja maganar ba, har sai abunda binciken ya gano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *