Yan sandan Abuja sun shiga daji farautar masu garkuwa

Spread the love

Rundunar ƴan sanda a Abuja, babban birnin Najeriya sun ritsa wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne a maɓoyarsu cikin dazuka da tsaunuka da ke kewayen Apo.

Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

Sanarwar ta bayyana cewa “jami’an rundunar ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ƴan sanda CP Benneth Igweh sun kai samame cikin dazuka da ke kewayen shiyyar Zone A da B na unguwar Apo domin tabbatar da matakan tsaro a yankin saboda ana ganin wurin ya zama maɓoyar masu sace mutane.

“Sumamen ya haɗa da ƙone gidajen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba da dazukan da ke kewayen tsaunuka da kuma tura ƴan sanda su yi rangadi a yankunan.

A cewar sanarwar, Igweh ya umarci mutane su ci gaba da taka tsan-tsan sannan su kai rahoton duk abin da zuciyarsu ba ta yi na’am da shi ba ga ƴan sanda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *