Yan sandan Adamawa sun cafke matashin da ake zargi da hallaka jami’in kotu bayan ya kai masa sammaci

Spread the love

Wani mutum mai shekaru 43 da aka kai wa takardar sammaci ya soka wa ma’aikacin kotun wuka ya kashe shi.

Mutumin ya yi wa akawun kotun wannan aika-aika ne a unguwar Kugama Wuro Jibir, Karamar Hukumar Mayo Belwa da ke Jihar Adamawa.

Ma’aikacin kotun mai suna Yauba Usman ya kai masa takardar sammaci ne daga kotun yanki na Nasarao Jereng, amma mutumin ya ki karba.

A maimakon haka, sai mutumin ya zaro wuka ya rika soka wa ma’aikacin kotun, ya ji masa raunuka, lamarin da ya sa aka kai shi asibiti, amma rai ya yi halinsa.

Kakakin ’yan sandan jihar Adamawa, SP Sulaiman Nguroje ya ce a sakamakon haka runduarsu ta cafke wanda ya yi wannan aika-aika, ana masa tambayoyi a ofishinsu.

SP Nguroje ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Afolabi Babata ya ba da umarni a zurfara bincike a kan lamarin.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *