Yan sandan Bauchi sun gano Bindigun da aka yasar a kusa da Kogi.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Bauchi ta samu nasarar gano wasu bindigu kirar AK47 da AK49 wadanda aka yasar da su a cikin wata jaka .

Kakakin rundunar yan sandan jahar Bauchi, SP Ahmed Muhammed Wakil, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

SP Ahmed Wakil, ya ce rundunar ta samu bayanan sirri na ganin wata Jaka a kusa da Kogin Chika-Chika mai tazarar kilomita 200, da babbar hanyar Gida Dubu a yankin karamar hukumar Ningi ta jahar.

Bayan samun rahotannne kwamishinan yan sandan jahar CP Auwal Musa Muhammed, ya tura tawagar jami’an yan sandan karkashin jagorancin Baturen yan sanda na Ningi, zuwa wajen tare da gudanar da bincike.

Ya kara da cewa jami’an yan sandan sun gano bindigu kirar AK47 guda 2 sai kuma bindiga kirar AK49 guda 1 da kuma kwanson harsasai guda 9.

Kwamishinan yan sandan jahar CP A.M.Musa, ya yaba wa dakarun yan sandan, inda ya yi kira a gare su da kara jajirce wa wajen tattara bayan sirri da zai taimaka mu su, don dakile aiyukan batagari.

Rundunar ta ce yanzu haka ta fara gudanar da bincike kan bindigun da aka samu a bakin kogin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *