Rundunar yan sandan jahar Ekiti ta gurfanar da wasu mutane 2 a gaban kotun Majistiri dake jahar Ekiti kan zargin satar naira dubu tamanin da hudu da dari bakwai N84,700 a ranar juma’ar da ta gabata.
wadanda ake zargin sun hada da Oribamise Emmanuel da kuma Mohammed Tijani, bisa tuhumar su da aikata laifuka biyu a gaban kotun.
Mai gabatar da kara , Olumide Bamigbade, ya shaida wa kotun cewa sun aikata laifin ne tun a watan Nuwamban 2023 a yankin Oye-Ekiti.
Ya ce sun sace zunzurutun kudi naira dubu N54,000 mallakar Omotosho Funmilayo da kuma naira N30,700 mallakar Adeyemi Tawa.
Ya kara da cewa laifin da ake zargin su da aikata wa ya saba wa sashi na 302 karamin sashi na (1) (a) cikin baka na dokokin jahar Ekiti shekarar 2021.
Bayan karanto kunshin tuhumar da ake yi mu su nan ta ke suka musanta zargin.
Mai gabatar da karar ya roki kotun ta bashi wata rana don yaje yayi nazari kan tuhumar tare da gabatar da shaidu.
Lauyan wadanda aka yi kara, Kayode Oyeyemi, ya roki kotun ta bayar da belin su, tare da yin alkwarin cewar ba za su karya sharudan belin ba.
Mai shari’a Olubunmi Bamidele, ya bayar da belinsu kan kudi naira dubu hamsin N50,000 ko wannensu da kuma mutum daya wanda zai tsaya mu su , inda ya dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Fabarairun 2024