Rundunar yan sandan jahar Imo, tare da hadin gwiwar wasu Mafarauta sun kai sumame a maboyar masu garkuwa da mutane, a tsakanin dajin Avu da kuma Ihiagwa dake jahar.
Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jahar ASP Okoye Henry, ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a jiya Talata.
ASP Henry, ya ce an kai sumamen ne a ranar 29 ga watan Janairu 2024, bisa jagorancin kwamishinan yan sandan jahar CP Aboki Danjuma, inda suka samu nasarar kama mutane biyar da ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.
Mutanen da aka cafke, sun hada da Mu’azu Ahuta , Abdullahi Abubakar, Uzairu Sabo, Saddam Sulaiman da kuma Bashir Yahaya, dukkansu yan karamar hukumar Jahun ta jahar Jigawa.
An bai wa iyalan ‘yan sandan da suka mutu naira miliyan 135 a Zamfara
Iyalan yan sanda 88 da suka rasu sun karbi Chekin kudi sama da N40m a Kano.
Rundunar yan sandan jahar Imon ta kara da cewa, kafin su kai sumamen sun samu bayanan sirri kan wadanda ake zargin da suke cin karensu babu babbaka a dajin na Avu da kuma Ihiagwa.
ASP Okoye, ya kara da cewa , mutanen da aka cafke suna bayar da hadin kai wajen amsa tambayoyin da jami’an yan sandan ke yi mu su, kuma sun baza komarsu domin kamo masu hannu a aikata laifin.
Sanarwar ta ce an samu gawarwakin mutane biyu da ake kyautata zaton suna daga cikin irin mutanen da aka yi garkuwa da su sannan aka hallaka su, amma har yanzu ba akai ga gane ko su waye ba, inda kwamishinan yan sandan jahar ya ce za a tantance su ta hanyar gwajin DNA.
Sai dai an gano wasu kayayyaki da suka hada da, wayoyin salula, Takalma, Babura 5 da kuma Agogon hannu.
Rundunar ta ce , ta daura damarar fatattakar masu aikata laifuka a jahar, domin ba za su rintsa ba sai kawo karshen batagari.
A karshe rundunar ta ce da zarar ta kammala bincike zata gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci, daidai da laifin da ake zarginsu da aikata wa.