Yan Sandan Jahar Adamawa Sun Kama Matasa Uku Da Ake Zargi Da Aikata Fashin Wayoyin Al’umma

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Adamawa, ta samu nasarar kama wasu matasa uku da ake zargin ma su yin amfani da makami ne wajen jiwa al’umma raunuka, a yayin kwace mu su dukiyar da suka mallaka.

Wadanda ake zargin sun hada da Jamil Sunusi mai shekaru 19, Yusuf Sardauna mai shekaru 21 da kuma Ma’azu Abdullahi mai sheakru 20.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Adamawa SP Sulaiman Yahya Nguroje, ya tabbatar da cewa , wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu da aikata wa.

Binciken yan sanda na farko-farko ya tabbatar da cewa sun yi wa al’umma fashin wayoyin salularsu, ciki harda wayar wata daliba mai suna Lidia James dake karatu a jami’ar Modibbo Adamawa University Yola.

Sojoji sun kashe mayakan ISWAP biyar, sun kuɓutar da mata da yara a Borno

Aliko Dangote Ya Kaddamar Tallafin Buhunan Shinkafa Na Sama Da Naira Biliyan 15 Ga Mutanen Nigeria Miliyan 1

Matasan dai na amfani da wukake masu tsini da sauran makamai wajen tayar da hankulan al’umma da basu ji ba , ba su gani ba, a yankin Sangare Numan zuwa Wauro Jabbe dake jahar.

SP Sulaiman Nguroje, ya ce an kama wadanda ake zargin a ranar 22 ga watan Maris 2024.

Kakakin yan sandan jahar CP Dankombo Morris , ya bayar da umarnin gudanar da binciken kwakwaf , kafin daga bisani a gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci.

Dankwambo ya bukaci al’ummar jahar da su kasance ma su sanar da su dukkanin wani abu da ba su amince da shi ba, don daukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *