Yan Sandan Bauchi Sun Gurfanar Da Matashin Da Yake Yaudarar Samari Da Sunan Fatima Mai Zogale.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan Jahar Bauchi, ta gurfanar da wani matashi mai suna Kabiru Ibrahim, a gaban kotun shari’ar addinin musulinci mai lamba daya, bisa zarginsa da yin shigar Mata da sunan Fatima Mai Zogale, har yake yaudarar Samari.

An Kama Wanda ake zargin ne, a lokacin da yake kokarin cutar wani matashi kan cewar Fatima Mai Zogale ce, inda saurayin ya dauke shi domin yin kwanan gida amma da zuwansu ya gane cewar dan Uwansa Namiji ne.

Bayan gurfanar da shi a gaban kotun mai gabatar da Kara, ya karanto ma sa kunshin tuhumar da ake yi masa , inda nan ta ke ya amsa laifinsa.

Alkalin kotun mai Shari’a, Mallam Ibrahim Jibo, ya aike da shi zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa Ranar 30 ga watan Mayu 2024 kamar yadda jaridar idongari. ng, ta ruwaito.

Fatima Mai Zogale wata matashiya ce da shahararren Mawakin nan Dauda Kahutu Rarara, ya yi wa Waka , bayan ya siyi Zogale a Wajen ta a birnin tarayyar Nigeria wato Abuja.

Daga nan ne sunan Fatima Mai Zogale ya yadu a kafofin sada zumunta da kafafen yada labarai, har Mawakin ya Shirya Mata Wata liyafar ban girma a Wajen da aka kaddamar da Wakar Fatima Mai Zogale.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *