Yan sandan Jigawa sun cafke wadanda ake zargi da satar Awaki 48

Spread the love

Rundunar Yan Sandan Jihar Jigawa, ta kama wasu mutum uku kan zargin satar awaki 48 a Kananan Hukumomin Babura da Kiyawa na jihar.

Kwamishinan na yan sandan jihar, Ahmadu Abdullahi ne, ya shaida wa manema labarai a Dutse a ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ne, a wani samame daban-daban tsakanin ranar Litinin zuwa Talata.

Abdullahi, ya ce, biyu daga cikin su ana zargin su da hada baki da wani mutum wajen sace awaki 26, wanda kudin su ya kai Naira miliyan 1.3.

Wani mutum mai suna Hassan Ibrahim ne, daga kauyen Abari a Jamhuriyar Nijar, ya shigar da kara a ofishin ‘yan sanda na Babura a ranar 22 ga watan Janairu, cewar an sace masa awaki da kundinsu ya kai Naira miliyan 1.3.

Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, sun kai farmaki tare da kashe wasu kasurguman ’yan bindiga.

Ya ce rundunar, ta samu wasu bayanai lokacin da ta fara bincike, lamarin da ha kai ga cafke wani mutum da awaki takwas.

Kwamishinan, ya ce wadanda ake zargin bayan shiga hannu sun amsa laifin satar awaki 26.

Ya kara da cewa mutum na uku da ake zargi wanda mazaunin kauyen Dundubus ne a Dutse, an kama shi da awaki 22 da ake zargin na sata ne.

Kazalika, Kwamishinan ya ce za a gurfanar da su a kotu da zarar sun kammala bincike a kan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *