Yan Sandan Kaduna Sun Kama Mutane 3 Da Ake Zargi Da Satar Wayar Wutar Lantarki.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kaduna, ta samu nasarar kama wasu matasa uku da ake kyautata zaton suna da hannu wajen sata da lalata wayoyin wutar lantarki.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ce an kama wadanda ake zargin a kauyen Yanbita zuwa Panbegua dake karamar hukumar Lere ta jahar, inda aka samu nadin wayar wutar lantarkin a wajensu.

Jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa, wadanda ake zargin sun shaida wa yan sanda cewa su ma’aikatan wucin gadi ne, a ma’aikatar wutar lantarki ta Kaduna Electric, amma sun gaza gabatar da shaidar da zata tabbatar da hakan.

Binciken yan sanda na farko-farko sun gano cewar wani ma’aikacin gidan wuta na jahar Kaduna , mai suna Sunusi Yahaya, ake zargi da taimaka mu su wajen lalata wayar wutar lantarkin.

Shugabannin Majalisar Dattijai na nuna rashin adalci wajen jagoranci

Wata kotu ta yi umarnin a gabatar mata da Murja Kunya cikin munti 30 kacal a Kano

ASP Hassan ya kara da cewa, da misalin karfe 3:00pm na rana aka kama wadanda ake zargin lokacin da mataimaki na musamman ga gwamnan jahar Kaduna Sanata Uba Sani, ya kai ziyarar sanya ido kan aikin wutar lantarki a karamar hukumar Lere, inda aka ga matasan suna yunkurin yanke wayar lantarki.

Jaridar Idongari.ng, ta zaiyano sunayen wadanda ake zargin da Ibrahim Mu’azu ,Murtala Sulaiman da kuma Daniel Zakari , dukkansu yan shekaru 30.

Rundunar yan sandan ta ce ta dukufa wajen gudanar da bincike kuma da zarar ta kammala zata gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *