Yan Sanda Sun Kama Budurwar Da Ta Hada Kai Da Saurayinta Ayi Garkuwa Da Ita Don Karbar Kudin Fansa.

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Akwa-Ibom ta bayyana nasarar kama wasu batagari, ciki harda wata mata da ake zargi da hada baki da wasu maza hudu su yi garkuwa da ita.

Kwamishinan yan sandan jahar Waheed Ayilara wanda ya sanar da hakan ga manema labarai, ya ce sun Kama mutane 52, da ake tuhuma da aikata laifuka maban-banta.

Laifukan da ake zargin su da aikata wa sun hada da fashi da makami, aiyukan kungiyar asiri, damfara da safarar yara kanana.

Ayilara ya ce matan da suka kama yar asalin kauyen Nung Oku ne dake karamar hukumar Ibesikpo Asutan a jihar.

Ya ce dakarun Yan sandan sun kama ta bisa laifin hada baki da saurayin ta domin yin garkuwa da ita, har ta bukaci kudin fansa naira miliyan hudu.

Premium Times ta ruwaito cewa Yan sanda sun samu labarin garkuwar ne bayan wani Enobong Sampson ya sanar da jami’an Yan sandan cewa masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da yar uwarsa kuma sun bukaci naira miliyan hudu kudin fansa.

Dole sai an zakulo waɗanda suka kashe jami’an mu – Lagbaja

Dangote feeds 10,000 people in Kano daily for Ramadan, distributes 1 million bags of rice nationwide

“Nan da nan jami’an mu suka fara gudanar da bincike tare da tattara bayanan sirri domin kamo mutanen.

“A ranar Talata dakarun suka kama matar tare da saurayinta a maboyar su dake Mbierebe Obio dake karamar hukumar Ibesikpo Asutan.

“Bayan sun shiga hannun jami’an tsaro, matar ta tabbatar da cewa ta hada baki da saurayin ta da wasu maza uku domin a yi garkuwa da ita.

Matar ta ce ta yi hakan ne domin ta samu kudi daga hannun goggonta dake zama a kasar waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *