
Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama wasu magidanta biyu da ake zargin sun kware wajen cutar da mutane, ta hanyar aikata laifukan da suka shirya , cikinsu harda wadanda suka kware wajen bude safin Facebook da sunan mata tare da Sanya hotunan mata don yaudarar maza da sunan soyayya.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga jaridar www.idonagari.ng.
Ya ce a duk lokacin da mutum ya fara magana da su, sai su bayar da nambar waya Kuma da zarar mutum ya kira sai yaji muryar mace , bayan sun chanja muryar namiji zuwa ta mace a karamar wayar da suke amfani da ita.
Sp Abdullahi Kiyawa ya kara da cewa, a cikinsu akwai wadanda suke bayyana kansu a matsayin jami’an yan sanda amma na bogi , Inda suke kama mutum da zarar yaje don haduwa da macen da suka yi waya da ita Amma sai ya ga mazan su fito sun rike shi, su ce masa matar aure yake kira.
- Miji ya yi yunƙurin kashe matarsa kan zargin maita a Kano
- Ƴansanda sun kama wani matashi kan zargin kashe mahaifiyarsa a Bauchi
Yan sandan bogin suna Neman kudi a wajen duk Wanda suka kama da sunan sasantawa, kuma sun tabbatar da cewa sun Yi wa mutane hudu ciki harda Wanda suka karbe masa wayarsa saboda bashi da kudi.
Wadanda aka kama sun hada da, Musbahu Sha’aibu Rijiyar Lemo da kuma Salisu Adamu Kurna, ya yin da sauran kuma suka gudu, da yanzu haka Ake ci gaba da gudanar da bincike a Kansu don kamo sauran.
Tuni dai wadanda suka zo hannun suka amsa laifinsu da cewar sune suke zuwa a matsayin jami’an yan sanda don kamo mutum, kuma sun karbi kudade a Hannun mutanen da tsautsayin ya fadawa.
Rundunar yan sandan jihar Kanon , taja hankalin mutane musamman wadanda ake Yi musu magana ta shafukan sada zumuntar Facebook, su dinga kula da wuraren da za su Kai kansu don kar su fada ga halaka.
Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio — Mijin Natasha
Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda