Yan sandan Kano sun bayar da mako guda ga mutane 52 su kai kansu bisa zargin garkuwa da mutane, miyagun laifuka a kudancin Kano

Spread the love
CP M.U. Gumel lokacin da ya ziyarci kwanar Dangora kan babbar hanyar zuwa Kaduna don tabbatar da tsaro

Rundunar yan sandan jahar Kano ta bayyana sunayen wasu mutane 52 da ake zargi da aikata laifukan garkuwa da mutane da kuma wasu da suke tsara yadda za a cutar da jama’a a yankin kudancin Kano.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel ne, ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki na Kwanar Dangora a karamar hukumar Kiru Kano.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce kwamishinan yan sandan, yaje karamar hukumar Kirun ne dake kan iyaka da jahar Kaduna, don tattauna wa kan matsalolin da suka shafi yankin na tsaro.

Kwamishinan yan sandan ya ce, yanzu haka suna da sunayen mutane 20 da ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane a yankin, inda ya bukaci al’ummar da su gane su.

Babbar hanyar zuwa Kaduna

Rundunar yan sandan ta yi kira ga wadanda ta lissafo sunayen su da su kai kansu gareta, idan ba haka ba kuma hukumomin tsaro su fara farautarsu a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo.

Cikin wadanda rundunar ke nema sun hada da mutane 20 da ake zargin su da aikata laifukan garkuwa da mutane a wasu daga cikin kananan hukumomin Kudancin Kano dake makotaka da jahar Kaduna.

1 .Amadu Gajale
2. Bawale Yar Mariya
3. Dahiru Yar Mariya
4. Shehu Bawale Yar Mariya
5. Nakamanda Ringim Iso
6. Baidu Dan Soshiya
7. Maman Musa Gabari
8. Dan Gurgu Kyarana
9. Alh. Yellow Kyarana
10. Hussaini Dan Gidan Idi Agric Dan Soshiya
11. Abdulkadir Kura Kaikazo
12. Dogo Dan Dunkule Kyarana
13. Sa’idu Dan Soshiya
14. Rabo Fulani Dan Soshiya
15. Abdullahi Auta Jahu
16. Basiru Bako Dan Soshiya
17. Suhu Ardo Masaje
18. Murtala Ardo Masaje
19. Bello Kyarana
20. Hussaini Alh. Auta.

Sauran sun hada da wadanda ake zargi da kara dagula lamuran tsaro da kawo rashin kwanciyar hankali ga al’umma wajen aikata muggan laifuka.

Kwamishinan yan sandan ya bayyana takaicin sa kan yadda wani mai suna Alhaji Ali , wanda yake zuwa wajen yan sanda don a saki masu laifi , inda kwamishinan yan sandan ya ce wannan ba adalci yake yi wa hukumomin tsaro ba, domin an kama mutum sai an buncika idan bashi da laifi sai a sake shi , amma Alhaji Alin shi ne yake matsawa jami’an tsaro dan su saki wadanda aka kama.

CP Gumel, Ya tabbatar da cewar idan bai chanja halinsa ba za su hada da shi, domin harkar tsaro ba abun wasa ba ne.

sauran mutanen da ake zargi sun fito daga yankuna daban-daban kamar haka.

1. Jafaru Gwada
2. Aminu Tudun Wada
3. Salisu Zaria
4. Ibrahim Garin Babba
5. Shake Garun Babba
6. Alhaji Ali of Dan Buda Gigan Barmo

UNGUWAR NADABO
7. Ibrahim Pastor Haruna Rai
8. Danbu
9. Gali Haruna Rai
10. Shamsu Mudi Kariya
11. Tibin Dan Ummaru
12. Ahmad Dan Gidan Ali Mazo
13. Dalam Dan Gidan Talle Magini.

SABUWAR ABUJA

14. Kwano Dan Gidan Sile Joga
15. Munzali Ummaru Bakanike
16. Ibrahim Makocin Saddiqu Dogara

17. Iliya Shitu Me Manja
18. Yahaya Kaura Hudu
19. Abba Na Malam Ya’u
20. Kada Dama Ruwa
UNGUWAR RIMI FILIN IDI
21. Jafaru Gwada Hayin Kunza
22. Yakubu Filin Idi
23. Mai Dubu-Dubu
24. Mi’iraji Mahauci
25. Shegiyar Kafa
26. Dan Kawu.

UNGUWAR RIMI MASALLACIN JUMA’A

27. Gaddafin Masallacin Juma’a
28. Yasir Dan Wala-Wala
29. Dattijai Dan Gidan Babangida Aluma
GIDAN KWANO
30. Auwalu Mahauci
GIDAN BARMO
31. Ibrahim Black
KARIYA
32. Tsalha Kariya.

Rundunar ta shawarci mutanen 52 , sukai kansu gareta cikin mako guda, idan kuma suka gaza yin hakan dukkan abubuwan da ake zarginsu da aikata wa ya tabbata gaskiya, inda rundunar za ta yi amfani da jami’an ta wajen farautarsu a duk inda suke.

Tuna dai al’ummar yankin Kwanar Dangora suka yi fatan samun nasara ga rundunar bisa yadda kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel , yake fadi tashin ganin an samu zaman lafiya da walwalar al’umma na yaki da aikata laifuka a fadin jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *