Yan Sandan Kano Sun Cafke Kasurgumin Dan Fashi Da Makami

Spread the love

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta sanar da cafke wani ƙasurgumin ɗan fashi da makami tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda biyu da kum alburusai 47.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun kuma samu kuɗi kimanin Naira miliyan 4.9 a hannun wanda ake zargin.

A ranar Litinin da misalin ƙarfe 2 na dare ne, wani mazaunin garin Yandadi a ƙaramar hukumar Kunchi da ke Jihar Kano, ya kai rahoton cewa ’yan fashi sun kai masa hari a gidansa, sannan kwashe masa kuɗi Naira miliyan 15.

Duk da tarzomar da ake fama da ita a Kano sakamakon zanga-zangar yunwa, kwamishinan ’yan sandan jihar, Salman Dogo Garba, ya bayar da umarnin bin sahun waɗanda suka aikata laifin.

Da misalin ƙarfe 6 na safiyar ranar Talata ne, ‘yan sanda suka kama ƙasurgumin ɗan fashin mai suna Hassan Iliya, mai shekara 35 mazaunin garin Alhazawa a ƙaramar hukumar Musawa ta Jihar Katsina.

Ya shiga hannun rundunar ne yayin da yake ƙoƙarin tserewa a kan babur.

An samu bindiga ƙirar AK-47 guda biyu tare alburusai 47 da kuma kuɗi har N4,986,000.00 a cikin wata jakarsa.

Rundunar ta ce a yanzu haka tana ci gaba da gudanar da bincike.

Saurari karin haske daga kakakin rundunar yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *