Yan sandan Kano sun cafke likitan bogi da saurayin buduwar da aka yi wa Allurar zubar da ciki har ta rasa ranta.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano ta samu nasarar cafke wasu matasa biyu da ake zargin su da hada kai wajen aikata laifin kisan kai.

Tun a ranar 2 ga watan Disamban shekarar da ta gabata ta 2023, wani mai suna Nura Balarabe, mazaunin karamar hukumar Tofa Kano, ya shigar da korafin wajen jami’an yan sanda , da cewar wanda ake zargi na farko mai suna Ukasha Muhammed mai shekaru 19, dake zaune a kauyen Langel , ya yi wa kanwarsa ciki mai suna Amina Bala mazauniyar kwanar Mahuwa Tofa Kano.

Nura Balarabe , ya kara da cewa, Ukasha ya hada kai da wani likitan bogi, mai suna Chideri Ugwu mai shekaru 24 mazaunin unguwar Lanbun Banki, inda ake zargin ya yi mata allura tare da bata magani dan juna biyun dake dauke dashi ya zube wanda hakan yakai ga ta rasa ranta.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa idongari ng , cewar wadanda ake zargin tuni suka amsa laifinsu .

Ana dai zargin likitan bogin Chideri Ugwu, da yi wa mata ma su dauke da juna biyu allurar zubar da ciki wanda hakan ke haifar da mummunan sakamako.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya ci alwashin ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu , domin ya ce , ba za su rintsa ba har sai sun magance dukkan aiyukan batagari a duk inda suke a fadin jahar.

Daga karshe rundunar ta ce da zarar ta kammala gudanar da bincike za ta gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *