Rundunar yan sandan jahar Kano, ta cafke wasu matasa 15 da ake zargi da satar motocin al’umma a fadin jahar.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata.
SP Abdullahi Kiyawa , ya kara da cewa sun samu nasarar dawo da motocin satar guda 20, da ake zargin an sace su ne daga wajen mamallakansu cikin watan da ya gabata .
Wannan nasara na zuwa ne, kan ci gaba da fadada sintiti a lungu da sako jahar Kano dan kakkabe aiyukan batagari, da kuma kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.
A karshe SP Abdullahi Kiyawa ya ce, Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel , ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan wadanda ake zargin, kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci.