Yan Sandan Kano Sun Cafke Matashin Da Ake Zargi Da Kunna Wa Mutane 24 Wutar Fetur A Masallaci.

Spread the love

Rundunar yan sandan Kano, ta cafke wani matashi mai suna , Shafi’u Abubakar , dan shekaru 38 a duniya bisa zargin sa da kunna wa mutane wuta bayan ya zuba Fetur , lokacin da suke sallar Asuba , a garin Gadan dake Karamar hukumar Gezawa.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Ranar Laraba.

Sanarwar ta ce sun samu kiraye-kirayen jama’a kan cewar wuta ta tashi da misalin karfe 5:20am na Asubashin Ranar Laraba, a wani masallaci dake kauyen Gadan Karamar hukumar Gezawa, a daidai lokacin da suke yin sallar Asuba, wadanda mutane da dama Suka samu ranuka.

Bayan samun rahotan ne Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya tura wasu jami’an yan sanda , wadanda Suka kware kan duk wani Abu da yake tashi kamar Abun fashewa da dai sauransu, karkashin jagorancin CSP Haruna Isma’il, da kuma Baturen yan sanda na Gezawa CSP Haruna Iliya, tare da ba su umarnin a gaggauta zuwa wajen da lamarin ya faru, dan ganin an yi abunda yakamata kamar yadda jaridar idongari.ng ta ruwaito.

SP Abdullahi Kiyawa, ya Kara da cewa, bayan sunje wajen ne , aka samu nasarar toshe ko’ina ,tare da gaggauta ceto mutane 24, inda aka garzaya da su Babban asibitin Murtala Muhammed, a Birnin Kano.

Rahotanni na cewa an kwantar da mutane 24, da Suka hadar da Manya guda 20 da kuma yara hudu.

Binciken yan sanda na farko-farko, ya tabbatar da cewar, an jefa wutar ce ta Hanyar amfani da man Fetur.

Kakakin yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce yanzu haka Wanda ake zargi na farko mai suna Shafi’u Abubakar, an Kama shi, kuma ya tabbatar da cewa shi ne yaje ya siyo man Fetur a gidan mai, sannan ya sanya a cikin Wata roba ya watsa a cikin masallacin ya kunna wuta, ta dalilin haka hannayensu biyu Suka kone.

Rahotanni sun bayyana cewa, hakan ya faru ne sakamakon rigimar cikin gida ta rabon gado, kuma da zarar an kammala gudanar da bincike za a sanar da al’umma halin da ake ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *