Yan Sandan Kano Sun Cafke Matashin Da Ake Zargi Da Yi Wa Wani Mutum Yankan Rago.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta samu nasarar kama wani matashi, mai suna Abba Garba wanda akafi sani da ( Kuda) bisa zarginsa da hallaka Zaharaddin Iliyasu, ta hanyar yanka wuyansa wukar Zarto sakamakon sun samu sabani da marigayin.

Kakaki rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da jaridar idongari.ng, da yammacin ranar Asabar.

Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne a yankin Sabontitin Phanshekara karamar hukumar Kumbotso dake jahar, tun a daren ranar Juma’a 29-3-2024.

SP Kiyawa, ya ce jami’an yan sandan Panshekare ne suka samu nasarar cafke matashin, a lokacin da yake kokarin guduwa jamhuriyar Nijar .

Yanzu haka dai ya na tsare a hannun yan sandan domin ci gaba da amsa tambayoyi kafin a gurfanar dashi a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *