Rundunar Yan sandan jahar Kano, ta cafke mutane 178 cikin watanni biyu kachal , da ake zargi da aikata laifuka maban-banta.
Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattauna wa jaridar Idongari. ng, a birnin Kano.
Cikin jerin mutanen da rundunar ta Kama , sun hada da wadanda ake zargi da aikata laifin fashin da makami su 10, masu garkuwa da mutane 11 da chanjin kudaden waje ba bisa ka’ida ba, Dilolin kwaya 25, Barayin motoci 25, Yan Daba 65 da kuma Barayin Babura Masu kafa uku su 5.
CP Gumel ya Kara da cewa, sun yi nasarar tseratar da mutane 4 wadanda aka Yi garkuwa da su da kuma mutane biyu da aka Yi safararsu.
Kotu ta haramta bincike kan Ganduje game da bidiyon dala
Gwamnatin Enugu ta kashe kaji 30,000 a yayin rusau
Rundunar Yan sandan jahar Kano, ta Yi nasarar kwato bindigu kirar AK47 guda 2, bindiga kirar gida 1, Harsasai ma su rai na bindiga kirar Pump Action guda 4 Motaci 4.
Sauran sun hada da babura masu kafa biyu guda 10, Adaidaita sahu 3 , Shanu 56, Tumaki 90, Wukake 18 Adduna 12 da .kuma Dan Bida 5 .
” Maganar Daba babu ita a jahar Kano, domin har wake-wake naji Ana Yi a cikin gari; na kanji su babu sauran daba a Kano.
Kwamishinan Yan sandan ya godewa Matasa da yadda Suka rungumi kudirin zaman lafiya, kuma ya ce suna tare da su ba za a manta da su, domin gwamnatin jahar Kano, ita ma tana yin Nata kudire-kudiren alkairi wajen Samar mu su da aiyukan yi.
Rundunar ta ce ta gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin Yi mu su hukunci.