Yan Sandan Kano sun cafko mutum na 2 da ake zargi da laifin garkuwa da kuma kisan kai

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta bayyana shirin ta na gurfanar da Matasan nan su biyu a gaban kotu, bisa zarginsu da aikata laifin Garkuwa da karamin yaro sannan suka hallaka shi bayan sun nemi kudin fansa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullah Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aike wa da manema labarai a birnin Kano a ranar Laraba.

SP Abdullah Haruna Kiyawa, ya ce abun takaicin kuma Mara dadin ji , da ya faru tun a Ranar 12 ga watan Fabarairu 2024 , inda ake zargin wani mai suna Isma’il Adamu mai shekaru 22 dake Unguwar Mariri , da hallaka wani Yaro mai suna Abdullahi Sani mai shekaru 14 a duniya.

Cutar sanƙarau ta kashe ɗalibai 20 a Yobe

Jagoran Lauyoyin da Ya jagoranci maka Ado Gwanja, Badamasi.S.Gandu a Kotu bayan Rera wakokin ASOSA da Chass Ya Magantu.

Bayan jami’an yan sandan sun Yi nasarar cafke shi , ya shaida mu Su cewar sun aikata laifin ne da wani mai suna Ismail Rabi’u Wanda akafi sani da Risi.

Tun daga wancan lokacin ne yan sanda suka shiga farautar Risi domin cafke shi kan zargin da ake Yi mu Su.

Binciken yan sanda na farko-farko , ya tabbatar da cewa dukkan wadanda ake tuhumar sun amsa laifukan Su , kuma da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da Su a gaban kotu.

Kwamishinan Yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya hori jami’an yan sandan da su kara zage damtse wajen ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, tare da shawartar jama’a a duk lokacin da suka wani Abu da ba Su amince da shi ba, Su Yi gaggawar sanarwar a ofishin Yan sanda mafi kusa don daukar matakin da ya dace.

IDONGARI.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *