
Rundunar yan sandan jihar Kano, ta fara gudanar da bincike kan wani mai yawo yana tallan Kifi a unguwanni, bisa zarginsa da nuna wa barayi gidajen da suke shiga su yi sata.
Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jihar SP Abdullahi Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan ga jaridar www.idongari.ng , inda ya ce yanzu haka sun karbi korafe-korafen mutane da dama kan batun.
Rundunar ba ta bayyana sunan mutumin da ake zargin ba, sai dai ta ce shekarun sa sun kai 50, kuma yana da aure harda yaya.
Al’ummar unguwar Dorayi Jakada , ne suka yi nasarar kama mutumin sannan suka dankashi a hannun jami’an yan sanda don fadada bincike akansa, sakamakon yawaitar shiga gidajensu da ake yi lokacin da suke bacci , inda ake sace musu kayayyaki masu muhimmanci.
- Hukumar KSCPC Ta Ce Za Ta Yi Aiki Da Kafafen Yada Labarai Don Tsaftace Harkokin Siye Da Siyarwa A Kano.
- Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano
Mutumin da ake zargi ya shaidawa yan sanda cewa akalla ya nuna wa batagarin gidaje 95, a unguwar Dorayin, inda suke shiga su yi sata sannan su bashi wani abu daga cikin abubuwan da aka sata.
SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa wanda ake zargin yana fakewa da tallan Kifi a Baho , inda yake gane gidajen mutane ciki harda wadanda suke siyan Danyen Kifin a wajensa.
Tuni al’ummar yankin suka fara yin tururuwa zuwa shelkwatar rundunar yan sandan Kanon, don shigar da kokensu kan mutumin da ake zargin yana ba wa barayi sirrin gidajen jama’ar unguwar ta Dorayi.
Kawo yanzu da rundunar yan sandan bata yi Karin bayani ba, kan adadin batagarin da ta samu nasarar cafkewa.
A karshe rundunar ta ce da zarar ta kamala gudanar da bincike za ta gurfanar da mai Tallan Kifin , a gaban kotu don ya fuskanci hukunci daidai da laifin da ake zargin sa da aikata wa.