Biyo bayan takaddamar
ta kunno kai tsakanin majalissar dokokin jahar Kano da kuma shugaban karamar hukumar Gwale , Hon. Khalid Ishaq Diso , inda ta dakatar da shi , tun a watan Satumba 2023 bisa zarginsa da yin gaban kansa ta hanyar siyar da filayen gwamnati.
Tunda fari dai kansilolin karamar hukumar 6 ne cikin 10 suka kai korafin shugaban karamar hukumar ga majalissar dokokin jahar Kano, da cewar abubuwan da shugaban karamar hukumar ya ke yi sun saba ka’ida.
A baya shugaban majalissar dokokin jahar Kano, Hon. Jibrin Isma’il Falgore , ya sanar da dakatar da Ishaq Diso , tsawon watanni 3 tare umartar mataimakin shugaban karamar hukumar ya karbi ragamar mulkin har sai an kammala bincike.
To sai dai wata kotu ta yi umarnin shugaban karamar hukumar ya koma bakin aikin sa, sakamakon cika wa’adin dakatarwar da aka yi masa na watanni uku ya cika.
Tun cikin daren Larabar nan, aka samu tashin wata gobara da ta yi sanadiyar konewar ofisoshi 17 a sakatariyar karamar hukumar ta Gwale.
Rundunar yan sandan jahar Kano , ta ce tunda sanyin safiyar ranar laraba ta jibge jami’an yan sanda , hadin gwiwa da DSS da Civil Defence domin tabbatar da tsaro a yankin.
Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kara da cewa , wasu matasa sun yi yunkurin shiga harabar sakatariyar karamar hukumar , har sai da jami’an tsaron suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye suka tarwatsa su.
Sanarwar ta ce , kulawar wajen ta na hannun jami’an tsaron , dan sanya ido kan dukkan batagarin da ke yunkurin haifar da matsala, ya yin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
Kakakin hukumar kashe gobara reshen jahar Kano Saminu Yusuf Abdullahi , ya tabbatar faruwar lamarin, inda ya ce ofisoshi 17 suka lalace tare da konewar motoci guda uku.