Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta gargadi iyaye da su kula da tarbiyar yayan Su musamman yan kasa da shekaru 15, don dakile Su daga fada wa aikata laifuka.
Mai magana da yawun rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin Wani faifen bidiyo kamar yadda Idongari.ng , ta ruwaito.
Wannan dai na zuwa ne bayan fitar Wani faifen bidiyo a shafukan sada zumunta, inda aka hango Wani Yaro mai suna Abubakar Kabir dan shekaru 14 a duniya, ya na yin kirari irin na mafarauta da kuma dura ashariya.
Lamarin dai ya girgiza rundunar Yan Sandan da sauran al’ummar da suka ci karo da faifen bidiyon a safukan sada zumunta, Wanda ya Kai ga Kwamishinan yan sandan Kano CP Salman Dogo Garba, ya bayar da umarnin memo Yaron da kuma mahaifinsa, don dakile Yaron daga fada wa Aiyukan batagari.
- Ganduje Da Matarsa Za Su Bayyana A Kotu Kan Zargin Almundahana
- NCAA za ta hukunta kamfanonin jirgin sama da ba su mutumta ƙa’idar lokaci
SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya Kara da cewa, sun kadu sosai da ganin karamin yaron yana daga makami tare da yin ashariya, Wanda alamu Suka tabbatar da cewar ya na yin mu’amula a cikin wadanda suke shaye-shaye da kuma Aiyukan Daba.
Yaron dai ya tabbatar wa da Jami’an yan sanda cewar shi ne , a faifen bidiyon da ya yadu a shafukan sada zumunta, amma tsautsayi ya sanyi aikata wa.
Sai dai ya ce babu Wanda ya koya masa a a wayar hannu ya koya , lokacin da yake kallon yadda ake Yi.
Mahaifin Yaron Kabir Abdullahi, ya bayyana ransa kan wannan lamarin, tare da cewar duk danginsu babu Wanda yake harkar Gangi .
Yaron Mazaunin kwaryar birnin Kano, ne inda ya tafi karamar hukumar Kura taron Wani biki Wanda aka gudanar da kidan gangin acan har aka Yi masa faifen bidiyo.
Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta ce idan aka bar irin wadannan yara suna kwaikawiyon abunda wasu ke Yi , ba tare da an dauki mataki cikin gagga wa ba, babbar matsala ce ga al’umma ma Su taso wa.