Yan sandan Kano sun gurfanar da mutanen da ake zargi laifin kisan kai, kashe shanu a ricikin manoma da makiyaya a Bagwai.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano ta gurfanar da wasu mutane a gaban kotun Majistiri dake zaman ta, a Unguwar Norman’sland , bisa zargin su da aikata laifin kisan wani Makiyayi mai suna Shehu Abubakar, da kuma Bazama mu su shanu masu yawa.

Wadanda ake tuhumar sun hada da Sani Abdullahi Sarkin Ƴa, Iliyasu Isah, Sule Sa’idu, Isiyaku Ya’u, Rabi’u Sale da kuma Na’Alla Sani da kuma karin wasu mutane uku da ake nemansu.

Ana zargin su da hada kai wajen aikata laifi , barna da kuma Kisan kai , wanda ya saba da sashi na 97, 329, 221.

Tunda fari ana zargin sun farwa Makiyaya a garin Ƴa dake kamar hukumar Bagwai , inda suka kashe mu su Shanu guda 67 tare da tsoratar da guda 91, masu kimar kudi Naira miliyan dari da biyu da dubu dari bakwai (102.7m) sannan suka kone Babura 9 da kuma kisan da ake zargin sun yi wa Makiyayin.

Bayan karanto mu su kunshin tuhumar da ake yi mu su , dukkansu sun musanta zargin.

Mai shari’a Talatu Makama, ta dage ci gaba da sauraren shari’a har zuwa ranar 20 ga watan Disamba 2023 , inda ta yi umarnin a tsare su a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *