Yan Sandan Kano Sun Gurfanar Da Shamsiya Da Gungun Matasan Da Aka Kama Su Tare Da Zargin Satar Wayoyi

Spread the love
Bompai Logo

 

Rundunar yan sandan Jahar Kano, ta bayyana cewa ta sake kama Karin mutane 4 tare da kwato wayoyin sata 12 da ake zargin suna cikin gungun mutanen da matashiyar nan mai suna Shamsiya Adamu ta ke jagoranta.

Kakakin rundunar yan sandan Jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai a ranar Talata.

A ranar 2 ga watan Janairun 2025, rundunar  yan sandan Kanon, ta yi holen matashiyar mai suna Shamsiyya da ake zargi da ƙwarewa wajen satar wayoyi a unguwanni daban-daban a sassan Jahar, bayan shafe  shekara guda ana farautar ta.

”Shamsiyya ta ƙware wajen ɓullo da dabarun yaudara daban-daban don hilatar mutane wajen sace musu wayoyi”.

Kiyawa ya ƙara da cewa wadda ake zargin kan yi aiki ne tare da wasu mutu huɗu da ke taimaka mata ciki har da ɗan adaidaita sahu da mai cire musu kudi a cikin wayoyin da suka sata.

”Ƙwararriyar mai yaudara ce da ke shiga gidajen matan aure tare da sace musu wayoyinsu da kuma yin amfani da wayoyin wajen sace musu kuɗaɗen daga asusun ajiyarsu na banki.

Tuni dai aka gurfanar da Shamsiyya, da kuma gungun matasan da aka kama su tare bisa zarginsu da hada kai da shiga ta laifi da kuma sata , a gaban kotun majistiri mai lamba 18 dake zamanta a Gyadi-gyadi, inda kotun ta bayar da umarnin a tsare su a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya.

Karin mutane hudun rundunar yan san ta sake kamawa sun hada da Fati Auwal, Kamal Sale, Usman Nasir da kuma Bashir Ibrahim, da yanzu haka suke hannun jami’an yan sanda don gudnar da bincike bisa zarginsu da aikata sata da kuma siyan kayan sata.

 

SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa sun karbi  korafe-korafen mutane 86 kan gungun mutanen da suke satar wayoyin al’ummar musamman a gidajen mata aure da kuma wuraren sana’o’insu.

A karshe Kiyawa ya ce,  kwamishinan yan sandan Jahar CP Salman Dogo Garba, ya bayar da umarnin ci gaba da fadada bincike don dawo da sauran wayoyin salular da aka sace.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *