Rundunar yan sandan jahar Kano bisa jagorancin kwamishinan ta CP Muhammed Usaini Gumel, ta taya al’ummar jahar murnar nasororin da aka samu na wanzar da zaman lafiya a shekarar da ta gabata ta 2023.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a , na rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis.
Sai dai ya ce shekarar 2023 an fuskanci matsalar yan daba , a kananan hukumomi 8 na birnin Kano da fadan Manoma da makiyaya da kuma rigingimun siyasa da daidai sauransu.
Rundunar ta ce an samu laifukan garkuwa da mutane da kuma yunkurin da yan bindiga ke yi na shigowa ta kan iyakokin kananan hukumomin Kano.
Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana cewar nasarorin da suka samu ya biyo bayan umarnin da babban sufeton yan sandan Nijeriya IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya bayar kan dakile aikata laifuka a fadin jahar.
Kwamishinan ya godewa sauran hukumomin tsaro, malaman addini, masu ruwa da tsaki , kwamitin aikin tsaro da al’umma da kuma al’ummar jahar Kano.
Kwamishinan yan sandan ya kara da cewa sun samu nasarar gurfanar da wadanda ake zargi aikata laifukan garkuwa da mutane, fashi da makami, dillacin kwayoyi su 2,931.
Sai dai ya ce yan daba 662 sun tuba tare da ajiye makamansu a shekarar da ta gabata 2023.
A shekarar 2023, rundunrar ta cafke wadanda ake zargi da aikata fashi da makami 337, masu garkuwa da mutane 55, dilolin miyagun kwayoyi 65, barayin motoci 68, barayin adaidaita sahu 57 da kuma barayin Babura 76.
Sauran sune wadanda ake zargi da laifukan sata 178, yan damfara 59 da kuma yan daba 2,036.
Rundunar ta samu nasarar tseratar mutane 25 da ake yi garkuwa da su tare da ceto mutane 63 da aka yi yunkurin safararsu zuwa kasashen ketare.
Haka zalika an samu nasarar kwato bundiga kirar AK 47 guda 4 , SMG Rifle 1, Barretta pistol 3, Anti Riot 1, Double Barrel 8, Makarov pistol 2 , Pistol 5 , bundigu kirar gida 53, bindigar harbin tsintsaye 14 da bindigar wasan yara 14 sai kuma harsasai masu rai 83 dai dai sauransu.
Rundunar yan sandan Kano, ta kwato motocin sata 205, Baburan adaidaita sahu 34 da Babura masu kafa biyu 86 da kuma wayoyin salula guda 3,079 .
A bangaren dabbobi rundunar ta kwato shanun sata 64, Tumaki 35 da dai suransu.
Haka zalika an kwato katan 990 na maganin da lokacin amfani da su ya kare, sinki-sinki na tabar wiwi 2,051 da kuma kulli-kulli 3,630.
Kwalaben codeine 543, Diazepam , Exol Tablets 1,878 , Tramadol 2,050 da robar Sholusho 2,371.
Sauran sun hada da kwace wukake guda 2,127, Adduna 96 da Barandami, tsitaka da Danbuda.
An kuma kwato katunan cirar kudi na banki ATM guda 2,790
Kwamishinan yan sandan ya ce matakan da suka dauka sun haifar da da mai ido wajen tabbatar da tsaron al’umma da dukiyoyinsu .
Ya kuma godewa al’ummar jahar da kafafen yada labarai bisa hadin kan da suke bayar wa a koda yaushe .
Ko kiran rundunrar ta wadannan hanyoyi dan sanar da ita wani abu da ba a amince da shi ba , ko kawo daukin gaggawa
08032419754, 08123821575, 09029292926, Facebook: Kano State Police Command
Twitter: Kano State Police Command (@KanoPoliceNG)
Instagram: Kano State Police Command
Tiktok: Kano State Police Command.
Log NPF Rescue Me Application .
WWW.IDONGARI.NG