Yan Sandan Kano Sun Gurfanar Da Wanda  Ake Zargi Da Halaka Mahaifinsa Da Fatanya.

Spread the love

 

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta gurfanar da wani matashi mai suna Manu Umar Adamu, bisa zarginsa da dukan mahaifinsa, Adamu Usaini , da Fatanya wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.

Lamarin ya faru ne a garin Kunshama, dake karamar hukumar Rano Kano, a lokacin da wani riciki ya hada su da mahaifinsa.

Sai dai ana zargin shima marigayin Adamu Usaini, ya yi amfani da wata wuka inda ya sokawa dan nasa akansa.

Mai gabatar da kara ta shaida wa kotun cewa sabuwar tuhuma ce, kuma  ta roki kotun majistirin, ta bayar da umarnin karanto tuhumar da ake yi wa matashin, amma saboda rashin hurumi ba ta bukaci amsar sa ba.

Ana zargin matashin da laifin kisan kai karkashin sashi na 224.

Alkaliyar kotun mai shari’a Rakiya Tanko , ta dage shari’ar zuwa  ranar 22 ga watan Oktoba 2024 , don jiran shawarwarin gwamnati, inda aka aike da shi zuwa gidan ajiya da gyran hali da tarbiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *