Rundunar yan sandan jihar Kano, ta gurfanar da wasu mata biyu, a gaban kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Danbare , karkashin jagorancin mai shari’a Munzali Idris Gwadabe, bisa zarginsu da hada kai wajen aikata laifi da kuma bata suna, wanda hakan ya saba da sashi na 121 da 188 na dokokin shari’ar Penal Code.
A ranar 22 ga watan Fabarairun 2025 wata mai suna Murja Usman, ta garzaya ofishin yan sanda, inda ta yi korafin matan da suka hada da Usaina Isah da kuma Jamila Habibu dukkansu mazauna unguwar Rimin Auzinawa Kano, wadanda suka je har gidan ta a ranar 10 ga watan Fabarairun 2025, suka shaida mata cewar, wai ita maiya ce kuma ita ce ta yi sanadiyar barin cikin da Jamila Habibu ta ke dashi kamar yadda aljanunsu suka shaida mu su.
Bayan gurfanar da su an karata mu su kunshin tuhumar da ake yi mu su, wadanda dukkansu suka musanta zargin.
Alkalin kotun mai shari’a, Munzali Idris Gwadabe, ya Sanya wadanda ake zargin a hannun beli sakamakon daya daga cikin su bata da lafiya sabo da barin cikin da ta samu tare da dage shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Afrilun 2025 kamar yadda idongari.ng ta ruwaito .
- Yan Sanda Sun Tsare Jami’in Da Ya Harbi Jami’in Hukumar Shige Da Fice
- Muna da fetur ɗin da zai ishi Najeriya gaba ɗaya – Dangote