Rundunar yan sandan jahar Kano, ta kama wani matashi mai suna Auwalu Muhammed, mazaunin unguwar Rimin Kebe, bisa zarginsa da damfarar al’umma ta hanyar karbe mu su babur da sunan jami’in dan sandan.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani faifen bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook kamar yadda idongari.ng ta ruwaito.
SP Abdullahi Kiyawa, ya ce wanda ake zargin yana tare mutanen da suke da Babura, inda yake shaida mu su cewar sun aikata laifi, har ya bayyana musu cewa nambar da ke jikin Baburin nasu an daina amfani da ita, harma da wadanda ba su da namba a baburansu.
Daya daga cikin wadanda aka damfara ta hanyar guduwa da baburinsa, ne ya shigar da korafi a ofishin yan sanda, bayan wanda ake zargin ya nemi kudi har naira dubu biyar amma bai samu ba hakan yasa ya tafi da babur din.
” bayan ya tare ni sai ya ce mun namba ta bata da kyau, ya dauke ni akan babur dina muna zuwa ofishin yan sanda na nasarawa bai shigar da ni ba, har ya nemi na bashi naira dubu biyar sai na ce masa babu sai dai duba daya amma yaki karba wai sai na bashi dubu uku, hakan yasa ya tafi da babur din wai na zo na karba a ofishin yan sanda na Nasarawa kuma bayan na je aka ce mun ba a kawo babur ba”.
- PERSONNEL WELFARE: CP SALMAN DOGO GARBA DECORATES 154 TRAFFIC WARDEN WITH NEW RANK
- Babban layin lantarkin Nijeriya ya sake daukewa
Kiyawa , Ya ce bayan samun rahotanne kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Salman Dogo Garba, ya bayar da umarnin yin bibiya ta hanyar tattara bayanan sirri don kamo wadanda ake zargin da kama jama’a su gudu da baburansu.
Matashin da ake zargi ya shaida wa yan sanda cewa tabbas ya aika laifin amma wannan shi ne karon farko da ya taba aikata hakan, kuma shi ba jami’in dan sanda ba ne, amma jami’in kwansitabulare ne ( Dan sandan Sarauniya).
Tuni dai rundunar yan sandan jahar Kanon , ta ce duk wanda yasan maatshin ya taba aikata masa irin wannan damfarar ya je ya shigar da korafinsa, a shelkwatar rundunar dake Bompai ko kuma ofishin yan sandan Nasararawa ko ta nambar waya 07014601313, kuma da zarar ta kammala gudanar da bincike za ta gurfanar da shi a gaban kotu don ya fuskanci hukunci.