Yan Sandan Kano Sun Kama Mace Da Yunkurin Fitar Da Motar Sata Kirar Hillux Jamhuriyar Nijar

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano ta gano wata mota tare da kama wata matashiya mai suna Adama Hassan da ake zargi da yunkurin fitar da motar daga Nijeriya zuwa  Jamhuriyar Nijar.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta ce an kama Adama Hassan, a jihar Gombe lokacin da take yunkurin daukar motar don fita da ita.

Tunda farko ana zargin wani mutum da satar motar a karamar hukumar Fagge Kano, inda jami’an yan sanda suke farautarsa.

Rundunar yan sandan takarbi rahotan satar motar daga wajen mamallakinta a ranar 29 ga watan Satumba 2025, da cewar an sace masa mota Toyota kirar Hillux main amba ,GWA 998 AR, bayan haka ne yan sanda suka fara gudanar da bincike har aka kama mace da kuma kwato motar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *