Yan Sandan Kano Sun Kama Masu Tare Hanya Suna Neman Trending

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta samu nasarar kama wasu mutane su 7 wadanda dukkansu matasa ne harma da kananan yara, bisa zargin su da tare hanyar shatale-talen gidan gwamnatin jihar Kano, suna daukar bidiyo don su yada a shafukan sada zumunta.

 

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ya tabbatar da kamen a shafin sa na facebook a ranar jama’ar nan.

 

Daman dai a baya rundunar yan sandan jihar Kanon, ta gargadi irin matasan da suke tare hanya suna daukar faifen bidiyon don suyi suna a shafukan sada zumunta wato Trending, da su daina domin rundunar ta ce ba zata bari ana shiga hakkokinsu wasu ba don biyan bukatar kashin kai.

 

Wannan lamari dai yana damun jama’a, inda a wasu lokutan matasan kan shinfida Katifa ko tabarma inda suke kwanciya akan titin yayin da wasu kuma har wanka suke yi ko dafa abinci wanda hakan ke sanya masu ababen hawa tsayaa cak.

 

Tuni wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam suka yi Alla wadai da irin wannan dabi’i ta wasu matasa da suka kira rashin hankalin da rashin sanin abinda yakamata su yi.

Zuwa yanzu dai matasan da aka cafke suna hannun jami’an yan sandan jihar Kano, amma babu wani cikakken karin haske da rundunar yan sandan ta yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *