Yan sandan Kano sun kama matashin da ya hallaka abokin aikinsa da wasu mutane 13 kan yunkurin kone kamfanin Fas Agro.

Spread the love

    James Sama’ila wanda ake zargi.

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta tabbatar da cafke wani matashi mai suna James Sama’ila, mai shekaru 32, bisa zarginsa da hallaka abokin aikinsa mai suna Tukur Adamu Yusuf mai shekaru 32, wadanda suke aiki a kamfanin buhun Fas Agro dake Sharada Ja’en Kano.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ne ya tabbatar da hakan da yammacin ranar Lahadi.

Kiyawa, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30am na safiyar lahadi, bayan sun samu kiran neman kai daukin gaggawa.

Wani dake aiki a kamfanin ya shaida wa Idongari.ng, cewar fada ne ya barke, inda ake zargin James, ya shake wuyan marigayin tare da bubbuga masa wani karfe a ciki wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, ya kara da cewar bayan samun labarin ne kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya bayar da umarnin kai shi , Asibitin Murtala Muhammad dake birnin Kano, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

James Sama’ila, ya shaida wa yan sanda cewar shi ne ya aikata laifin, amma ya yi da na sanin zuwansa Kano.

Haka zalika rundunar ta ce ta kama wasu fusatattun matasa 13, da ake zargi da yunkurin satar kayan jama’a da kuma yunkurin kone Kamfanin.

 

Bayan sallar Lasa’ar ne aka yi Jana’izar mamacin a unguwar Dango Ja’en, cikin alhini da jimamin abunda ya faru.

An dai jibge tarin jami’an tsaro kan hanyar Sharada tare da rufe hanyar shiga kamfanin na Fas Agro, da wasu sassan lunguna dake yankin.

Da safiyar yau dai matasa sun gudanar da zanga-zangar luma a bakin kamfanin, inda suka zargi mahukuntan kamfanin da yin buris da kin kai matashin asibiti tunda wuri.

Yanzu haka dai al’amura sun lafa a unguwar , amma dai ana cikin jimami na rashin matashin mai matar aure daya da kuma kananan yara biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *