Yan Sandan Kano Sun Kama Mutane 2 Da Zargin Yi Wa Yan Kasuwar Beruit Satar Wayoyi A Shagunansu

Spread the love
SP ABDULLAHI HARUNA KIYAWA

 

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta yi nasarar kama wasu matasa biyu, wadanda ake zargi da aikata laifin satar wayoyin yan kasuwar Beruit Kano da kuma sayarwa.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna kiyawa , ne ya bayyana hakan hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa da idongari.ng, a karshen makon da muke ciki.

Sanarwar ta ce tun a ranar 22 ga watan Feabarairun da ya gabata 2025, yan kasauwar wayar suka yi nasarar kama daya daga cikin matasan mai suna, Tasi’u Ibrahim, mazaunin unguwar Sheka, a lokacin da suka shiga wani shagon siyar da wayoyi, amma ake zargin sun bige da yin sata, inda suka cafke Tasi’u Ibahim, bayan dayan ya gudu da wayar da satar.

Haka zalika a bibiyar da jami’an yan sandan suka yi ne, suka kamo wanda ake zargi da siyan wayoyin satar mai suna, Abduljabbar Musa Sheka, ake ci gaba da gudanar da bincike akansu kafin a gurfanar da su a gaban kotu.

Rundunar yan sandan taja hanakalin mutane musamman yan kasuwa da su kara kula sosai da masu zuwa yin sayayya a shagunan su, kasancewar ana samun batagarin da suke yaudararsu ta hanyar daukar kayansu ba tare da sun sani ba.

‘’ ka kula sosai kar ace ka dauko wani abu kafin ka juya an sace maka wani abu.

A karshe kuma rundunar ta ce idan akwai masu shagunan da aka yi musu sata ta irin wannan shigar, da su gaggauta kiran wadanda suke yin bincike kan korafin ta lambar waya kamar haka 07031666661.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *