Yan Sandan Kano Sun Kama Mutane 3 Da Zargin Kisan Kai Don Su Mallaki Takaddun Fili.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan jahar Kano ta cafke wasu matasa Uku da ake Zargin sun hada Kai tare da halaka Wani mutum mai suna Dahiru Musa , Dan Shekaru 32 mazaunin unguwar Dorayi.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike da Idongari.ng a ranar Laraba.

Ya ce tun a ranar 29 ga watan Satumba 2024, suka sami korafin bacewar Dahiru Musa , Inda kwamishinan yan Sandan jahar Kano CP Salman Dogo Garba, ya bayar da umarnin a Yi kokarin yin bibiya don Nemo mutumin.

Bayan Kwana daya ne Ake Zargin Wani yaron sa Mai suna Aliyu Adamu , shi ne Wanda suka Yi wayar karshe kuma yaje wajensa, Inda jami’an Yan Sanda suka kamo Aliyu Adamu.

Binciken Yan Sanda na farko-farko ya Kai ga kama karin mutane biyu da ake Zargi, da suka hada da, Mubarak Abdussalam Mandawari da kuma Dan adaidita sahu Mai suna Sadik Sunusi Mandawari.

Rahotanni na cewa wadanda Ake Zargin sun kira Dahiru Musa, ne bayan sun yaudare shi zuwa unguwar Yankusa a yankin karamar hukumar Kumbotso Kano, gidan Wanda Ake Zargi na farko har suka bashi Abinci Mai Guba ya ci Fita Daga Hayyacinsa.

Kakakin Yan Sandan Kanon , ya kara da cewa bayan da ya fara yin Amai sakamakon cin abinci Mai Gubar, sai suka dauko wukake suka dinga Caka masa har sai da suka tabbatar ya dai na motsi.

Daganan suka dauki Gawar marigayin suka sanya a cikin Buhu suka jefar da ita a cikin Wani Kango.

Haka zalika Wanda Ake Zargin na farko ya turo matarsa Unguwa, kuma bayan faruwar lamarin sun wanke gidan da ruwa don kar agane abunda suka aikata.

Haka zalika ana zargin sun Yi amfani da man Fetur wajen Kone Gawar.

Rundunar Yan Sandan ta ce dukkan wadanda Ake Zargin sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikata wa.

Daya Daga cikin matashin ya shaida wa, idongari.ng, cewa sun Yi hakan ne domin su dauke wata Takaddar filin marigayin da ya siya a unguwar Gaida don su siyar su raba kudin a Tsakanin su.

Yanzu haka dai suna babban sashin gudanar da binciken manyan laifukan kisan CID dake shelkwatar Yan Sandan a unguwar Bompai kuma da zarar an kammala bincike za a Gurfanar da su a gaban Kotu.

A karshe Rundunar taja hankalin al’umma da su kasance ma su kula d irin mutanen da za su Yi mu’amula da su, domin ba kowa Ake gasgatawa ba musamman wadanda suke kiran mutum zuwa wani kebantaccen wuri da a dinga tafiya da Yan rako.

Saurari muryar kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa da kuma Wadanda Ake Zargin..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *