Yan Sandan Kano Sun Kama Mutane 6 ,Wayoyin Sata 15 Da Adaidaita Sahu 2.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano ta samu nasarar kama wasu mutane 6 da ake zargin sun addabi sassan birnin jahar, tare da kwato baburan adaidaita sahu 2 da ake zargin suna amfani da su, da kuma wayoyin sata 15 da aka kwato daag wajensu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a jiya Alhamis.

Sanarwar ta ce an kama wadanda ake zargin ne daga ranar 11 zuwa 15 ga watan Janairun 2025, bayan samun bayanan sirri kan maboyar batagarin a sassan birnin Kano.

Wadanda ake zargin sun hada da, Bashir Isah, Isyaku Bala, Mudansir Ayuba, Muzambil Abdullahi, Ibrahim Mohammed da kuma Hassan Sagir.

SP Kiyawa ya kara da cewa, dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifinsu da cewa sun kware wajen satar wayoyin fasinjojin da suke dauka a baburansu na adaidaita sahu.

Baburan guda biyu suna dauke da nambar , KBT-850WZ da kuma DAL-113WZ sai wayoyin salula 15 da rundunar ta kwato daga hannunsu.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Salman Dogo garba, ya yaba wa jami’ansa bisa kwarewar da suka nuna yayin kai sumamen kamo wadanda ake zargin tare da yin kira ga al’umma su ci gaba da ba su hadin kai .

A karshe rundunar ta bayyana cewa duk wanda ya gane wayarsa ko baburin adaidaita sahu cikin kayan da rundunar ta kama ya garzaya ofishin kakakin rundunar yan sandan Kano, don yin haske ko kuma a kira 07063407910

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *