Rundunar yan Sandan jahar Kano, ta samu nasarar kama miliyoyin Dalolin kasar Amurika da Nairar Nigeria da kuma sauran kudaden ketare, da Ake Zargin na bogi ne (Fake) don cutar da Yan kasuwa .
Mai magana da yawun Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ( Bawahala) ne ya tabbatar da hakan ga Freedom Radio Kano, a ranar Lahadi 8 ga watan Disamba 2024.
Rundunar ta ce yanzu mutanen da Ake Zargi da kuma makudan kudaden suna hannunsu, Inda Ake ci gaba da lissafa su.
- Hukuncin Kisa Ne Ya Dace Da Masu Kashe Jamiāan Tsaro : Babangida Aliyu
- An Kai Wa Mahaifiyar Gwamnan Jihar Taraba Da Yar Uwarsa Hari.
SP Abdullahi Kiyawa, yaja hankalin Yan kasuwa, da su kara Sanya Ido , kan dukkan kudaden Ake kawo mu su don kaucewa fada tarkon mayaudara.
” Yan kasuwa a kara sa Ido, irin wadannan mutanen da muka kama da kudade a wajensu, ba su kadai ba ne , duk Wanda ya zo siyayya da makudan kudade na farko a samu Kwararru su duba kudin musamman wadanda suke chanja Dala” SP Abdullahi Kiyawa “.
Ya kuma gargadi irin mutanen da ba su Dala, ba idan an kawo mu su , su nemi masani ya duba mu su don gudun fadawa matsala.
Rundunar Yan Sandan ta kara da cewa , Zargin da suke Yi shi ne za a dinga shigar da kudaden bogin kadan-kadan zuwa Kasuwanni.
A karshe Rundunar ta ce ta na ci gaba da gudanar da bincike, kuma ba za ta gajiya ba , wajen ci gaba da wayar da kan al’umma daga wannan almundahana.