Rundunar yan sandan jahar Kano, ta kama wasu mutane uku da aka samun jabun Kudi, a wajen su kimanin naira Biliyan 129 da miliyan 542 da kuma naira 824 ( N129,542,824,000:00: ).
kudaden da aka samu a hannun wadanda ake zargin sun hada da jabun Dalar Amurka, CFA da kuma Naira.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake holen wadanda ake zargin a shelkwatar rundunae dake unguwar Bompai.
SP Kiyawa ya ce sun samu nasarar kama mutum na farko mai suna Ahmad Abdullahi, dan shekaru 30 mazaunin karamar hukumar Kaga ta jahar Borno, bayan samun sashihan bayan sirri, inda kwamishinan yan sandan jahar, CP Salman Dogo Garba, ya tura dakarun yan sanda karkashin jagorancin SP Abdurrahim Adamu , baturen yan sandan Gwale, don fadada bincike kan lamarin.
Tun a ranar 1 ga watan Disamban 2024, rundunar ta fara kama wani mai suna Nura Ibrahim Sharada da kuma Muhammad Muktar Hotoro, inda bincike ya kai ga kamo wanda ake zargi da mallakar kudin jabun mai suna Ahmad Abdullahi.
Jaridar www.idongari.ng, ta ruwaito cewa, mutane daga cikin mutanen da ake zargi sun shiga gidan wanda ake zargi na farko da nufin yin sata, har suka ga jabun kudaden a cikin wasu jakunkuna inda su kuma suka fara neman wadanda za su chanja mu su kudin zuwa naira hara aka kama su.
SP Abdullahi Kiyawa ya kara da cewa jabun kudin da aka kama za a dinga yin amfani da su wajen damfarar yan kasuwa ta hanyar shigar da su kasuwanni kadan-kadan.
A karshe ya ce da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci