Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bankaɗo wasu miyagun ƙwayoyi, da darajar kudin su ta kai sama da Naira miliyan 42, tare da cafke wasu fitattun mutane da ake zargi da aikata laifin fashi da makami.
Wannan na cikin sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce, a wani samame da aka gudanar, jami’an rundunar sun cafke, Nura Sani mai shekara 20 dan jihar Bauchi da kuma Ibrahim Lawan mai shekara 35 dan jihar Katsina, bisa zargin yin fashi ayankin Tokarawa Quarters ranar 14 ga Satumbar daya gabata.
An yi zargin cewar sun ƙwace motar Mercedes Benz GLK mai darajar Naira miliyan 26.5m da wayoyi da sauran kayayyaki.
- Siyasa Da Tsaro: Gwamnan Kano Ya Tura Neman A Sauya Kwamishinan Yan Sandan Jihar.
- Sarkin Kudan Ya Taya Mai Martaba Sarkin Zazzau Murnar Cika Shekaru 5 Akan Karagar Mulki.
Haka kuma, a Jalli dake karamar hukumar Dawakin Tofa, an gano fakiti 540 na maganin Pregabalin da darajarsu ta kai naira miliyan 40.5m.
Haka zalika a ranar 30 ga Satumba 2025 an kama wani mai suna Alhaji Isyaku Babayo Kofar Mazugal da Mohammed Ahmed Dorayi Babba a unguwar Trailer Park, Dangauro, dauke da jakunkuna 7 na ruwan maye “Akuskura” jimilla kwalabe 2,450.
Yanzu haka dai rundunar ta miƙa miyagun kwayoyin ga hukumar NDLEA, domin ci gaba da bincike kafin a gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.