Rundunar yan sandan jahar Kano ta cafke wasu mutane 4 bisa zargin su da aikata laifin buga takaddun kammala makarantun na bogi.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga, idongari.ng, a ranar Litinin 30 ga watan Satumba 2024.
Kiyawa ya ce bisa rahotannin sirrin da suka samu, ne suka yi nasarar kama mutanen da suka hada da, Idris Yahaya, mai shekaru 42 mazaunin Gandun Albasa , Umar Abba, mai shekaru 52 mazaunin Zangon Bare-bare, Jibrin Sani, mazaunin Jakara da kuma Ahmad Ado Iliyasu, mazaunin Mandawari dukkansu a jahar Kano, wadanda ake zargin sun kware wajen buga takkadun bogi na manyan makarantu da kanana tare da siyarwa al’umma.
Binciken yan sandan ya gano wasu takaddar na jami’a da na shaidar kammala kwalejojin ilimi da na lafiya , Shaidar bayar da gurbin karatu admission letters, NYSC da kuma takaddar mallakar filaye duka na bogi.
Tuni dai wadanda ake zargin suka amsa laifin da ake zarginsu da aikata, inda rundunar ta ce da zarar ta kammala za ta gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.
- Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin kula da marayu 95
- Budaddiyar Wasika Ga Gwamnatin Najeriya (An Bar Jaki Ana Dukan Taiki Akan Lafiya)