Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kuɓutar da wata ƙaramar yarinya mai shekara huɗu daga hannun masu garkuwa da mutane tare da kama wanda ake zargi da sace yarinyar.
Cikin wani saƙo jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce a ranar Talata jami’an ‘yansanda suka kama wani matashi mai suna Saifullahi Abba, mai shekara 23, bisa zargin garkuwa da yarinyar.
Tun da farko mahaifin yarinyar ne mai suna Zilkiflu Abdullahi da ke zaune a ƙauyen Dakatsalle a yankin ƙaramar hukumar Bebeji ya kai wa ‘yansanda ƙorafin sace ‘yar tasa mai suna Nabila a ranar 22 ga watan Nuwamban da muke ciki.
”Kwana guda bayan haka kuma sai wani mutum ya kira shi tare da iƙirarin sace ‘yar tasa, sannan ya buƙaci naira miliyan uku a matsayin kuɗin fansa”, kamar yadda SP Kiyawa ya bayyana.
‘Yansandan sun ce sun kama wanda suke zargi da sace yarinyar – wanda ɗan asalin ƙaramar hukumar Wudil ne – a ƙauyen Luran da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu.
”Wanda ake zargin ya amince da laifin da aka tuhume shi, sannan ya jagoranci jami’an ‘yansanda zuwa inda ya ɓoye yarinyar a ƙauyen na Luran, inda nan take aka kuɓutar da ita,”Kamar yadda kakakin ‘yansandan jihar Kanon ya bayyana.