Yan Sandan Kano Sun Kubutar Da Yaron Da Aka Yi Garkuwa Da Shi Tare Da Kama Wadanda Ake Zargin

Spread the love

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta samu nasarar cafke wasu mutane 3, da ake Zargi da yin Garkuwa da Wani karamin yaro Dan Shekaru hudu a duniya, wadanda suke Nemi kudin fansar naira Miliyan 10.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da manema labari a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce , an Yi Garkuwa da yaron Mai suna Muhammed Nasir Jamilu, mazaunin Sharada Kano, a ranar 7 ga watan Satumba 2024, Inda suka Kai shi maboyarsu dake karamar hukumar Gwarzo Kano, har suka karbi naira Dubu dari Uku, Kafin a cika mu su ragowar kudin.

Wadanda Ake Zargin sun hada da Hisbullah Salisu mai Shekaru 30 da Hassan Ali Rabi’u mai Shekaru 28 dukkaninsu mazaunan unguwar Yakasai, sai kuma Hassan Ali mai Shekaru 22 da mazaunin unguwar Hotoro kuma tuni jami’ansu sun cafke su.

Binciken Yan Sanda na ya tabbatar da cewa Wanda Ake Zargi na farko ya ce ya hada Kai da mutenan biyu, Inda Sace Dan Yayansa Mai shekaru hudu.

Bayan ceto yaron an Kai Asibitin Murtala Muhammed Kano, don duba lafiyarsa kuma tuni aka mika shi Hannun iyayensa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *