Yan Sandan Kano Sun Shawarci Masu Yin Bidiyo Rike Da Makami Su Kai Kansu Wajen DPO Yankin su

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta bayyana cewa rike makami a dauki faifen bidiyo tare da yYada shi, a shafukan sada zumunta laifi ne.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce daman tuni kwamishinan yan sandan jihar CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarmin kamo duk Wanda aka gani yana yada faifen bidiyon rike da makami a shafukan sada zumunta.

A cewar daman tuni sun kama wani matashi da ake yi wa lakabi da LINGA kuma ana zarginsa da koyar da fadan daba, a shafin TIKTOK da sauran su.

Haka zalika rundunar ta shawarci wadanda suka san sun dauki faifen bidiyon rike da makami su hanzarta Mika su ga baturen ƴan sandan yankinsu.

Yawancin matasan da suke daukar bidiyon suna rike da Adduna ko Takobi harma da Gorori suna koyar da daba ne da Kuma kwace da haura gidajen jama’a don aikata Sata.

 

SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa kowa yasan abinda zai Yi na daidai da kuma mara kyau , kuma ana samun wannan matsala ne saboda sakacin wasu iyaye kan yayansu.

Sai dai rundunar ta yaba wa mutane unguwar Zango da Kofar Mata, kan Wani taron zaman lafiya da suka gudanar don kawo karshen fadan daba tsakanin wasu matasan yankin.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *