Yan sandan Kano sun tabbatar da mutuwar dan fashin wayar nan da mota karya wa baya

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar matashin nan da ake zargi da aikata laifin fashi da makami, da ya kwace wayar wata mata akan titin gidan zoo, inda Mota ta buge shi lokacin da yake kokarin tsallaka titi ya gudu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan a ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook

Kiyawa ya ce matashin ya mutu ne a safiyar ranar talata asibitin Murtala dake birnin Kano.

Tunda da fari dai Matashin ya kwace wayar matar ce, bayan yayi mata barazana da Danbuda, kuma yana kokarin guduwa mota ta takashi ta karya masa baya har ya samu mummunan rauni akan sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *