Yan sandan Kano sun yi nasarar cafke yan fashin da suke satar motocin jama’a suna siyar wa a jamhuriyar Nijar

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano ta samu nasarar cafke wasu matasa da ake zargi da aikata laifin fashi da makami da satar Motocin al’umma.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Alhamis.

 

Ya ce an yowa matasan safarar wasu bindigu daga jamhuriyar Nijar zuwa jahar Kano domin su yi amfani da su, wajen cutar da al’umma da aikata fashi makami sannan su tafi da kayan zuwa Nijar suci ganima.

CP Gumel ya kara da cewa , tun a ranar 24 ga watan Disamba 2023, suka samu labarin cewar barayin sun mamaye wani gida a unguwar Sharada , har suka daure mai gidan mai suna Yusuf Baba Wapa da kuma mai gadinsa.

 

Yan fashin sun kwashe masa wayoyin salula da kuma motocinsa guda biyu masu kirar Toyota Rav4 2021 da Honda Accord .

Binciken yan sanda na farko-farko sun kai ga samun bayanan sirri, kan wadanda ake zargin har suka gano hanyar da suka bi, inda jami’an yan sanda suka yi amfani da karfi bayan sunki tsaya wa a Jibia dake jahar Katsina.

Jami’an rundunar yan sandan jahar Katsina , ne suka fara cafke wani mai suna Gambo Fahad , a Jibia ya yin da Nafi’ Umar , ya tsere tare barin motar da ya sato, a kokarin da suke yi na shiga da su jamhuriyar Nijar.

Wanda aka cafke din ya bayyana wa jami’an yan sandan cewar, akwai gungun yan fashi da suke yin Haya a wani gida dake Unguwar Rijiyar Lemo Kano, inda rundunar ta kai simame tare da cafke wani Sadik Isma’il.

Kwamishinan yan sandan Kano, ya ce sun yi nasarar samun bindigu kirar Beretta guda biyu a cikin gidan.

 

Dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifinsu tare da cewa, sun saci motoci da yawa wadanda suke siyar da su a jamhuriyar Nijar.

Sai dai kwamishinan ya kara da cewa, akwai wani Buzu da yanzu haka yake a jamhuriyar Nijar shi ne yake ba su makaman da suke aikata fashin.

Rundunar ta ce tana ci gaba bincike domin cafke Buzun dan ya fuskanci hukunci.

Tuni rundunar ta bayyyana cewa ta mayar wa da mai motocin kayan sa , kuma da zarar sun kamma bincike za su gurfanar da su a gaban kotu.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *