Rundunar Yan sandan jahar Kano, ta samu nasarar cafke wani matashi mai suna Mashkur Muhd Zango, mai shekaru 21 a duniya, Wanda ake zargi da Dillacin Tabar Wiwi a sassan birnin Kano.
Mai magana da yawun rundunar Yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani faifen bidiyo da ya aike wa da jaridar idongari.ng, a ranar Juma’a.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce Wanda ake zargin ya shafe kusan shekaru hudu, yana dillacin tabar Wiwin ga wasu gurbattun matasa.
Matashin ya shaida wa jami’an yan sanda cewa, yana haduwa da wasu abokansa Yan Unguwar Fagge, Zage da kuma Kofar Wambai .
Ya Kara da iyayensa sun San ya na siyar a tabar Wiwin , wadanda suka yi masa fadan siyarwa tun abaya amma yaki daina wa.
Sai dai ya ce , kudaden da yake samu wajen siyar da tabar Wiwin , a banza suke kashe kudin ba tare da yin wani abu da zai amfane shi ba.
- Basaraken Rivers da sojoji ke nema ya miƙa kan sa
- Kotu Ta Yanke Wa Mutumin Da Ya Haura Gida Ya Saci Dubban Dalolin Amurika Hukunci A Kano.
An dai samu nasarar kwace Wuka, Danbuda da Tabar Wiwi daga hannunsa.
Ya kuma tabbatarwa da Yan sanda cewa, suna yin amfani da makamin wajen yin barazana a duk lokacin da suka ga hukumar yaki da Hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ko jami’an Yan sanda , inda suke zarowa sannan su gudu.
Kakakin Yan sandan Kanon, ya ce matashin ya shaida mu su cewar , yana shan kayan maye da suka hada da , Sirop da tabar Wiwi.
Rundunar Yan sandan jahar Kano, ta tashi wajen yaki da Yan Daba , da kuma masu siyar da kayan maye, don kakkabe aiyukan su a fadin jahar Kano.