Rundunar ‘yan sanda a Legas ta ce ta kama kimanin mutum 400 da take zargi da aikata ayyukan bata-gari a sassan birnin, a watan Janairu.
Mai magana da yawun rundunar, SP Benjamin Hundeyin wanda ya tabbatar wa kamfanin labarai na Najeriya, NAN, ya ce sassan ‘yan sanda 25 ne suka aiwatar da aikin.
Kotu ta yanke wa mutumin da hukumar Hisbah ta kama tare Murja Kunya hukunci a Kano.
Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta Cafke Murja Ibrahim Kunya
Hyundeyin ya ce ya zama dole su kaddamar da babban samame bisa la’akari da irin korafe-korafen da jama’a ke kai musu da kuma bayanan tsaro da suka tattara.
Ya kara da cewa za a ci gaba da aiwatar da irin wannan tsarin domin tabbatar da an kakkabe baragurbi daga birnin na Legas