Yan sandan Najeriya sun hana amfani da sarar ”No gree for any body

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta haramta amfani da wata sara da mafi yawan matasan ƙasar ke amfani da ita ta ”No gree for any body” da ke nufin “kar ka ɗaga wa kowa ƙafa”.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ƙasar, Muyiwa Adejobi, ya ce an ɗauki wannan matakin ne saboda zargin cewa “sarar ta samo asali ne daga mutanen da ke son kawo juyin juya hali a Najeriya.”Tun da aka shiga sabuwar shekara ta 2024 ne dai matasa ke amfani da sarar

Adejobi, ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun ɗauki sarar a matsayin babbar barazana ga tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *