Yan sandan Najeriya sun kama gomman masu aikata laifuka

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce jami’anta da ke aikin wanzar da tsaro a kan titin Abuja zuwa Kaduna sun samu nasarar kama gomman mutanen da take zargi da aikata miyagunj laifuka.

Cikin wata sanarwar da rundunar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce jami’an rundunar da ke aiki a kan babban titin sun samu gagarumar nasara a aikin kakkaɓe ayyukan ɓata-gari a yankin.

Sanarwar ta ce jami’an ‘yan sandan sun kama mutum 81 da suke zargi da fashi da makami, da mutum 44 da suke zargi da yin garkuwa da mutane, sai mutum 73 da suke zargi da aikata laifin kisan kai, da mutum 36 da suke zargi da fyaɗe da mutum 22 da suke zargi da hannu a ayyukan da suka danganci tsafi ko asiri, da kuma wasu 28 da ‘yan sandan suka zarga da aikata sauran laifuka.

Yan sandan sun kuma ce sun gano bindigogi 16 da nau’ikan harsasai daban-daban, da kuma wasu muggan makamai fiye da 200.

Sanarwar ‘yan sanda ta kuma ce jami’an sun gano ababen hawa 28 da ake zargin na sata ne, da buhunan takin zamani kimanin 600.

Haka kuma ‘yan sanda sun ce sun gano tsabar kuɗi naira miliyan 3,350,000 da suka yi zargin cewa an biya kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane.

‘Yan sandan sun kuma ce sun samu nasarar kuɓutar da mutum 158 da aka yi garkuwa da su, waɗanda tuni ‘yan sanda suka ce an sada su da iyalansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *