Yan sandan sun gurfanar da wanda ake zargi da sare Danyatsan matashi da Adda a Kano.

Spread the love

Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a unguwar Gama PRP Kano, ta tsare wani matashi a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya, bisa zarginsa da samar da mummunan rauni, wanda laifin da ya saba da sashi na 159.

Tunda fari ana zargi Banbagida Sabo mai shekaru 24, da yin amfani da wata Adda, ya kaftawa Abubakar Yusuf Dakata, har ya datse masa Danyatsa.

Sakamakon hakan ne ya rasa Danyatsan sa daya a hannun dama.

Bayan faruwar lamarin ne ya garzaya wajen jami’an yan sanda ya yi korafin wanda ake zargin, su kuma suka gurfanar da shi a gaban kotun.

Mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa, inda ya musanta zargin.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed , ya bada umarnin tsare shi a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 8 ga watan Fabarairun 2024 dan gabatar da shaidu akansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *