Rundunar ƴan sandan Najeriya, shalkwatar Zone One da ke Kano, ta yi wa sanannen ɗan jarida mai gabatar da shirye-shirye, kuma shugaban sashin shirye shirye na musamman na Hikima Radio Ibrahim Ishaq, wanda aka fi sani da Ɗan’uwa Rano, tambayoyi bisa zargin ɓatanci da kuma gudanar da tashar talabijin ta yanar gizo ba tare da izinin Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Shirye-shirye ta Ƙasa (NBC) ba.
Binciken ya biyo bayan ƙorafin da Daraktan Al’amuran Fadar Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya shigar, inda ya zargi ɗan jaridar da ɓatanci da ɓata masa suna ta cikin rahotannin da ake yaɗawa a Dan’uwa Rano TV, wata kafar yaɗa shirye-shirye ta yanar gizo.
Rahotanni sun ce an gayyaci Ɗan’uwa Rano zuwa shalkwatar ƴan sanda ta Zone One a Kano a ranar Asabar, inda aka yi masa tambayoyi kan waɗannan zarge-zargen.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da bincike kan Mista Rogo, wanda ake zargin yana ƙarƙashin binciken Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) bisa zargin ɓarnar kuɗaɗe da suka shafi kwangiloli da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 6.5.
A halin yanzu, ƙungiyoyin ƴan jarida da na farar hula a Kano sun yi Allah-wadai da tambayar da aka yi wa Ɗan’uwa Rano, suna bayyana hakan a matsayin yunƙuri na tsoratar da kafafen yaɗa labarai da toshe muryoyin masu sukar gwamnati.